Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali- Soyayya Ta Yi Sanadin Mutuwar Budurwar Da Ta Cinnawa Kanta Wuta, Okotoba, 24, 2019


Alheri Grace Abdu

Ranar ishirin da tara ga watan Oktoba na wannan shekarar, Shirin Domin Iyali ya kawo maku labarin wasu masoya a Gusau babban birnin jihar Zamfara, da tsanannin soyayya ya sa budurwar zubawa kanta fetir ta cinnawa kanta wuta sabili da saurayinta bashi da halin daukar nauyin auren.

Wannan lamarin yarinyar ta shiga ya dauki hankalin al'umma da masu hali baiwa da suka yi alkawarin tallafawa masoya ta wajen daukar nauyin auren da duk dawainiyar jinyar .

To sai dai burin masoyan da ma duk wadanda suka ji wannan labari na daurawa masoyan auren ba zai cika ba sabili da Aisha ta cika jiya Laraba da safe a babban asibitin Gusau inda tayi jinya .

Saurari cikakken shirin.

Soyayya tayi sanadin mutuwar wata budurwa a Gusau-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:54 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG