Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU, DOMIN IYALI, Nuwamba 02, 2017: Rahoto Na Musamman Kan Aurar Da 'Yaya Mata Da Wuri


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

Shugabannin kasashen Canada, Malawi, Uganda da kuma Zambia, tare da hadin guiwa da asusun tallafawa kanananan yara UNICEF, da asusun kula da yawan al'umma UNFP, da kuma cibiyar tarayyar Afrika sun gudanar da wani zaman tattaunawa na musamman yayin taron kolin Majalisar Dinkin Duniya na saba'in da biyu, da nufin shawo kan aurar da 'ya'ya mata da wuri. Kiddidiga ta nuna cewa Jamhuriyar Nijar har yanzu ita ke kan gaba wajen aurar da 'ya 'ya mata da wuri a kasashen duniya, inda aka yi kiyasin cewa, ana yiwa kashi saba'in da shida cikin dari na mata aure kafin su cika shekaru goma sha takwas. Ta haka shirin Domin Iyali zai yi bibiya kan wannan matsala da nufin gano abinda ke haifar da daukar wannan matakin da illarta ga ci gaban iyali, da kuma matakan shawo kan matsalar

A Jamhuriyar Nijer kungiyoyi masu zaman kansu da hadin guiwar hukumomin kasar sun dukufa ga ayyukan fadakarda jama’a illolin dake tattare da dabi’ar aurarda ‘yan matan da shekarunsu ba su kai na aure ba, bayanda aka bayyana kasar a jerin kasashen da suka fi yiwa ‘yan mata auren wuri.

Bayanai na nunin mata kimanin 700 ne ke kamuwa da matsalar yoyon fitsari a kowace shekara a jamhuriyar Nijer. Aurarda ‘yan matan dake da karancin shekaru na kan gaban a dalilan dake janyo wannan matsala. Yawaitar wannan matsala dake takaita sha’anin karatun ‘yan mata ya sa kungiyoyi masu zaman kansu irinsu DIMOL kaddamar da ayyukan fadakarwa da na jinkai domin ceto rayuwar ‘yan mata da suka fada irin wannan ukuba.

Gargadi da jan hankulan jama’a a game da ililolin dake biyo bayan aurarda ‘yan mata masu karancin shekaru wani aiki ne da‘yan majalisar dokokin kasar nijer ke ganin suna da gudunmowar da zasu bayar domin cimma nasara akansa. Masana a fannin halittan jikin dan adam sun bayyana cewa shekaru 18 da haifuwa sune aka tabbatar a matsayin na cikar budurcin ‘yan mace saboda haka kungiyoyin masu zaman kansu suka dukufa ga wajen gudanar da ayyukan wayar da kan al’umma dangane da mahimmancin mutunta wannan sharadi da dokokin kasar nijer suka gindaya.

Fifita al’adun gargajiya da kuma addini na daga cikin dabi;un da wadansu mutane ke labewa da su domin aikata abubuwan da ke cutawa rayuwa duk kuwa da cewa malamai sun sha kwatantawa jama’a da a kaucewa yin irin wannan shigshigi mafari kenan da kungiyar WILFAD reshen NIJER ta soma tuntubar samari da ‘yan mata domin su gane illolin rungumar al’adar da ba ta da amfani duniya da lahira.

Wasu matasan da shirin ya tantauna da su akan matsalar auren wuri sun bayyana cewa a halin yanzu kan mage ya waye.

Alkaluman kididiga sun yi nuni da cewa Sama da kashi 52 daga cikin 100 na al’umar nijer dukkansu mata ne haka kuma bayanai ke nunin sama da kashi 70 na yawan jama’ar kasar matasa ne, yayinda masana ke cewa yankunan MARADI da ZINDER ne ke kan gaba wajen aurarda yara kanana saboda dalilai masu nasaba da matakin kare ‘yan mata daga matsalar daukar cikin shege.

Ga rahoto na musamman da wakilinmu Sule Mummuni Barma ya hada mana.

Auren da 'Yaya Mata da Wuri-10:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:39 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG