Accessibility links

GRACE ALHERI ABDU, Domin Iyali: Satumba 21, 2017- Hira da Frederica Wilson

  • Grace Alheri Abdu

Yar majalisar dokokin Amurka Frederica Wilson da Grace Alheri Abdu

Makon da ya gabata gwamnatin tarayyar Najeriya tayi bukin sallamar ‘yammatan Sakandaren Chibok dari da shida da kungiyar Boko Haram ta saki bayan garkuwa dasu na tsawon shekaru uku. Gwamnatin tarayya ta ajiye ‘yammatan a wata cibiya dake birnin tarayya Abuja domin kula da lafiyarsu da kuma taimakonsu su iya fuskanta rayuwar yau da kullum. Kafin gudanar da wannan bukin wata tawagar ‘yan majalisar dokokin tarayyar Amurka karkashin jagorancin Frederica Wilson sun kai ziyarar gani da ido a Najeriya. Bayan dawowarsu kuma nayi hira da ‘yar Majalisa Frederica wadda ta fara da bayyana makasudin zuwanta Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG