Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Satumba 13, 2018: Rayuwar Kunci Da 'Yan Jamhuriyar Nijar Ke Shiga A Saudiya


Grace Alheri Abdu

Yau shirin Domin Iyali ya nazarci rayuwar mata ‘yan Jamhuriyar Nijar a kasar Saudiya inda suke tafiya da nufin neman ingancin rayuwa sai dai idan suka isa wurin su tarar ba haka lamarin yake ba

A wani yunkurin kare ‘yan Nijar dake aikatau a kasar Saudiya Hukumomin jamhuriyar ta Nijar sun dakatar da dukan wasu tafiye tafiyen matan dake zuwa Saudiya da sunan sana’ar aikatau bayan da bayanai suka tabbatar da cewa mata ‘yan Afirka na fuskantar gallazawa daga mutanen da suka daukesu aiki yayinda masu kare hakkin dan adam a na su bangare ke ta zumudin samun damar zuwa wannan kasa domin ganewa idanuwansu zahirin abinda ke faruwa daga bakin wadanda wannan al’amari ya sama.

Shirin Domin Iyali ya gabatar da muryar wata mata da jama’a suka yi ta aikewa juna kenan ta wayar telephone a matsayin daya daga cikin matan Nijar dake aikatau a kasar Saudiya.

Matar ta nuna kosawa da bakar azabar da suke fuskanta daga wajen mutanen da suka daukesu aiki ta hanyar wasu kamfanonin samar da aikin yi .

Kungiyoyin kare hakkin jama’a musamman masu kare muradun mata sun yi wa wannan al’amari ca sakamkon yawaitar irin wadanan koke koke na neman ceto da nuna nadamar shiga aikatau.

Domin tabbatarda gaskiyar lamari ministan kwadagon Nijar Ben Omar ya ziyarci kasar ta Saudiya inda suka gana da mata ‘yan Nijer masu aikatau. Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam na ganin akwai bukatar shigar da su cikin wannan yunkuri na hukumomi

A ci gaba da neman hanyoyin haska fitila kan ayyukan kamfanonin dake dillanci tsakanin masu fatan a daukesu aikatau da attajiran Saudiya a dai gefen, gwamnatin jamhuriyar Nijar ta yanke shawarar dakatar da dukan wani shirin aika matan kasar zuwa Saudiya a hukunce har zuwa lokacin da za ta samu tabbacin daukar matakan mutunta hakkokin ‘yan kasar da suka je neman kudi .

Masu rajin kare hakkin jama’a sun yaba da wannan mataki saboda a cewarsu zai taimaka a saka tsari a wannan fanni da masana ‘yancin bila dama key iwa kallon sabon salon bauta.

Koda yake a shekarar 2017 wasu mata ‘yan nijer da aka yada bidiyonsu a kafar facebook sun karyata arahoton dake cewa ana gallazawa masu aikatau a Saudiya, rahotanni daga wannan kasa na cewa dimbin mata ‘yan Nijar ne suka nuna kosawa da halin da suke ciki a wuraren da suke aikatau saboda tsananin wahalar aiki da cin zarafi yayinda a wasu gidaje ake mayar da irin wadanan mata tamkar kilakai ba da amincewarsu ba lamarin da ya sa suka fara gane cewar gida tafi inda suka je neman ingancin rayuwa.

Saurari shirin a cikin Sauti

Rayuwar Matan Nijar A Kasar Saudiya-10:25"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:34 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG