Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Iyayen ‘Yan Matan Chibok Sun Kaure Da Murna A Dandalin Unity Fountain


'Yan Kungiyar BBOG A Dandalin Unity Fountain Don Murnar 'Yan Matan Chibok Da Aka Samo

‘Yan kungiyar BBOG sun kaure da murna a Dandalin Unity Fountain bayan labarin matan Chibok 82 da aka ceto sun shiga fadar shugaban Najeriya Aso Rock, inda suka gana da shugaba Buhari.

Duk da dai ba a baiwa ‘yan kungiyar damar su gana da matan da aka samo sun yi gangamin murna da wasu daga cikin iyayen matan.

Ester Yakubu, na daga cikin iyayen da ‘yarta Dokas ke cikin wadanda aka sace, wadda ta ce ko cikin ‘yan matan 82 babu ‘yar ta to tana taya sauran uwaye murna. Kuma idan babu ‘yar ta yanzu gaba insha Allahu za ta ta zata fita.

Shi kuma, Yusuf Sallau, ya nuna godiya da jin dadinsa ga shugaban ‘kasa ga wannan alkawari da ya cika, da kuma taya murna ga iyayen yaran da za su sami ‘ya ‘yansu.

Da take amsa tambayar wakilin Muryar Amurka, kan cewa me yasa kungiyar bata yabawa kokarin gwamnati ganin yadda ake samo ‘yan matan, sakatariyar kungiyar BBOG, Aisha Yusufu, ta ce idan har gwamnati ba tayi abin yabo ba babu yadda za a yaba mata.

'Yan Kungiyar BBOG A Dandalin Unity Fountain Don Murnar 'Yan Matan Chibok Da Aka Samo
'Yan Kungiyar BBOG A Dandalin Unity Fountain Don Murnar 'Yan Matan Chibok Da Aka Samo

Kasancewar kungiyar ta yi tsayin daka kan ganin cewa an ci gaba da tashi tsaye wajen nemo ‘yan matan da aka sace.

Shugaba Buhari wanda ya dauki hoto da ‘yan matan 82 cikin farin ciki ya nufi Landon don ci gaba da duba lafiyarsa.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG