Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guaido Na Kira Ga Sojoji Da Su Goyi Bayan Kaurace Wa Zaben Venezuela


Juan Guaido
Juan Guaido

Ga dukkan alamu shirin gudanar da zaben kasar Venezuela zai fuskanci cikas ganin yadda jagoran 'yan tawaye ke kiran sojoji su nesanta kansa daga shirin zaben.

Jagoran 'yan adawa a Venezuela, Juan Guaido na kira ga shugabannin soji na kasar da su goyi bayan kaurace wa zaben yan majalisu mai zuwa a ranar 6 ga watan disamba.

A wani jawabinsa da ya wallafa a shafinsa na twitter, Guaido ya ce yana matukar alfahari da kowane bangare na kasar, shi ya sa yake gayyatar soji da su zo a hada kai wajen hana gudanar da wannan zabe.

Ya ce tawagarsa za ta zauna da duk wandanda suke da yakinin goyon bayansa wajen aiwatar da wannan lamarin.

Tun lokacin da Guaido ya ayyana kansa a matsayin shugaban rikon kwarya a shekarar da ta gabata, bayan da ya zargi Maduro da tafka magudi a zaben shekarar 2018, Guaido dai ya kasa samun goyon baya a Venezuela wanda zai janyo hambarar da Maduro.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG