Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwa Da Ambaliyar Ruwa Sun Haddasa Matsaloli A Amurka


Guguwa A Amurka

Masu hasashen yanayi a Amurka suna jan hankalin jama’a dangane da matsalolin ambaliyar ruwa da za’a iya samu a tsakiyar kasar yau Talata.

Masu hasashen yanayi a nan Amurka suna kara jan hankalin jama’a dangane da matsalolin ambaliyar ruwa da za’a iya samu a tsakiyar kasar yau Talata.

Hukumar kula da yanayi ta bayyanar da cewar an samu matsananciyar guguwa a gabashin jihar Indiana da yammacin jihar Ohio a daren jiya, wadda ta lalata gidaje da hanyoyi.

Hukumomi na cigaba da nazarin irin barnar da guguwar tayi, amma dai har zuwa yanzu ba’a rasa rai ba.

Tun a makon da ya gabata ne ake ta fama da matsalolin ruwa da guguwa mai karfi a jihohin tsakaiyar Amurka, wanda aka rasa rayuka a cikinsu, wadanda suka hada da jihohin Missouri, Oklahoma, Iowa da Indiana.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG