Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janaral Buhari Yayi Wawan Kamu a Jihar Neja


Janaral Muhammad Buhari.
Janaral Muhammad Buhari.

Janaral Muhammad Buhari dan takarar shugaban kasa a karkashin APC ya kai ziyarar yakin neman zabe a jihar Neja.

Janaran wanda ya samu tarba daga dubun dubatan jama'a a Minna babban birnin jihar ta Neja ya sha alwashin tabbatar da inganta tsaro da samar da aikin yi ma 'yan Najeriya idan har aka zabeshi ya zama shugaban kasa.

Ziyarar ta Janaral Buhari ta kaiga jam'iyyarsa tayi babban kamu a jihar domin mataimakin gwamnan jihar Alhaji Ahmed Musa Ibeto da wasu magoya bayansa sun canza sheka sun shiga APC daga PDP.

Alhaji Ibeto ya bayyana dalilansa na barin jam'iyyar PDP zuwa APC. Yayin da jam'iyyarsa ta da wato PDP ta fitar da dantakarar gwamnan jihar Neja yace ba'a yi masa adalci ba kuma ya kai kuka ga uwar jam'iyyar amma bata biya masa bukata ba. Shi da magoya bayansa suka dauki shawarar barin PDP inda suka ce babu adalci.

To saidai a nata taron da ta gudanar a Kontagora domin kaddamar da yakin neman zaben Alhaji Umar Naskona PDP din gwamnan jihar Babangida Muazu Aliyu ya mayar da martani. Yace dama suna addu'a duk wanda zai kawo masu cikas Allah yayi waje dashi. To Allah ya amsa addu'o'insu da fitar Ibeto zuwa APC. Amma yayin da gwamnan Filato Jonah Jang ke jawabi a wurin taron inda yayi fatan PDP ta sake cin zabe, wasu matasa sai suna ihu suna cewa sai Buhari. Sai da 'yansanda suka yi anfani da barkonon tsohuwa kafin su shawo kan matasan.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG