Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Duoye Diri Na Jam'iyyar PDP Ne Ya Lashe Zaben Bayelsa - Kotu


Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri (Hoto: Shafin Duoye Diri Facebook)

Rahotanni daga Najeriya na cewa, kotun daukaka kara da ke Abuja, ta jingine hukuncin da wata kotun tribunal mai sauraren kararrakin zabe ta yanke, wanda ya soke nasarar da Gwamnan jihar Bayelsa Duoye Diri ya samu a zaben da aka yi a ranar 16 ga watan Nuwambar 2019.

A watan Agusta kotun da ke sauraren korafe-korafen zabe a Abuja ta soke nasarar Mr. Diri na jam’iyyar PDP tare da ba da umurnin a sake wani sabon zabe cikin kwana 90.

Kotun sauraren kararrakin zaben ta soke nasarar Diri ne bayan da jam’iyyar ANDP ta yi korafin cewa an cire ta a zaben.

Sai dai a hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, wanda ya samu goyon bayan daukacin alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a Adzira Mshelia, kotun daukaka karar ta jingine hukuncin na watan Agusta.

Hujjar da kotun daukaka karar ta gabatar na soke hukuncin kamar yadda rahotanni suka nuna ita ce, jam’iyyar ta ANDP ta shigar da korafinta a makare, sannan kotun ta tribunal da ke Abuja wacce ta soke zaben Diri a watan Agusta, ba ta da hurumin sauraren karar ta ANDP.

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG