Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Na Shida a Najeriya Da Covid-19 Ta Harba


gwamnan jihar delta, Ifeanyi Arthur
gwamnan jihar delta, Ifeanyi Arthur

Gwamnan jihar Delta a Najeriya Ifeanyi Arthur Okowa ya bayyana a yau Laraba cewa ya kamu da cutar Coronavirus.

Ya sanar da hakan ne a kan shafinsa na Twitter inda ya ce da shi da mai dakinsa ne cutar ta harba.

Gwamnan ya rubuta a shafin nasa cewa, "Muna cikin koshin lafiya kuma muna ci gaba da killace kanmu, da shan magani."

Gwamnan ya bukaci jama'a da su yi wa 'yarsu addu'a wacce itama take fama da cutar.

Shi ne dai Gwamna na shida da ya kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.

Gwamnan jihar Ondo
Gwamnan jihar Ondo

A jiya Talata ne gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa yana dauke da cutar shima.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG