Gwamna Ayodele Fayoshe yace lamarin abin takaici ne, bashi cikin ra’ayin kasar mu irin haka ya rika faruwa. Yace idan aka duba za’a ga cewa kasar Nigeria tafi rarrabuwa a cikin shekaru biyu da suka wuce, kuma wannan ba shine shugabanni irin su marigayi Tafawa Balewa da Dokta Nnamdi Azikiwe da Cif Obafemi Awolowo suke son gani ba.
A kan batun ballewar kabilar Igbo daga Najeriya, Gwamna Fayoshe yace wannan ba ra’ayin shugabanni mu na farko bane, amma ina son gwamnatin tarayya ta zama uba ga kowa, a saurare kowa a yi sulhu, saboda sulhu itace hanya mafi kyau na shawo kan kowa ce matsala. Zaman dardar ya yi yawa a Najeriya, ya kamata a zauna da al’umman Igbo a tattauna da su.
Da ya ci gaba da bayani, Gwamnar na jihar Ekiti yace yana nufin Najeriya ta kasance kasa daya. Yace ko a turai ana samun irin wadannan matsaloli, yayi misali da Northern Ireland da Britaniya, amma hanyar magance su sune a zauna ayi sulhu.
Yace a saurari kowa, gwamnatin tarayya ta kula da kowa. Gwamna Ayodele Fayoshe yace mafita itace gwamnatin Najeriya ta canza dabi’unta, Najeriya kasa ce mai kabilu da yawa kada a yi amfani da karfi a rufe bakin wasu jama’a. Gwamnan Fayose yayi wannan furucin ne a hirarsa da wakilin sashen Hausa Hassan Umaru Tambuwal.
Facebook Forum