Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Bauchi Da Abba Kyari Sun Harbu Da Cutar Coronavirus


A yayin da yawan wadanda suka kamu da cutar coronovirus ya kai 42 a Najeriya, gwamnan jihar bauchi dake arewacin kasar ya kasance gwamna na farko da ya kamu da cutar, wasu rahotanni a kafafen sada zumunta kuma na cewa babban jami'in fadar shugaban Najeriya Malam Abba Kyari shima ya kamu da cutar, bayan dawowar sa daga kasar Jamus.

Wannan na zuwa ne bayan da cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta ba da rahoton mutuwar mutum na farko sakamakon cutar coronavirus ranar Litinin 23 ga watan nan na Maris.

Hakazalika a ranar ta Litinin tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana cewa dansa, Mohammed Atiku Abubakar ya kamu da cutar coronavirus amma ana kula da shi a asibiti a yanzu haka.

Saurari karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG