Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Hana Kiwo A Ekiti, Ba Gudu Ba Ja Da Baya - Inji Fayose


Shanun Fulani Makiyaya

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yace dokar hana yawo da dabbobi a cikin jihar na nan daram.Yace an samar da dokar ce ba domin rukunin wasu mutane ba,amma ga dukkan 'yan jihar.

Yayin da ake kai ruwa rana game da samarwa makiyaya wurin kiwo a cikin jihohin Najeriya, Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yace dokar da ya kafa na hana kiwo barkatai nan nan daram.

Gwammnan ya furta hakan ne sailin da yake tattaunawa da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka, Hassan Umaru Tambuwal ta wayar tarho.

Fayose yace daya daga cikin abinda yayi game da wannan dokar shine ya tabbatar kowa nada rawar da zai taka game da wannan dokar, domin samun nasarar taga kowa da kowa.

Yace ya kafa dokar ce ba tare da jiran sai wani ko wasu sun mutu ba kafin ace a samar da doka, kuma wannan dokar ba anyi ta bane domin wasu rukunin jamaa sai domin masu aikata ayyukan assha koda kuwa da wani irin harshe suke magana.

Ga Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani: 3’37.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG