Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jigawa Ya Dakatar Da Kwamishina Kan Zargin Almundahana


Sabon Gwamnan Jigawa
Sabon Gwamnan Jigawa

Cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a, wadda sakataren gwamnatin jihar Jigawa Alhaji Bala Ibrahim ya sanyawa hannu, gwamman jihar Umar Namadi, ya bada umarnin dakatar da kwamishinan ciniki da masana’antu Alhaji Aminu Kanta, bisa zargin sa da hannu a almundahana.

Yayin da al’umar musulmi ke daf da kammala ibadar Azumin Ramadana, aiwatar da shirin gwamnatoci na ciyar da mabukata a cikin wannan wata na cin karo da kalubalen zargin almundahana, inda ake tuhumar wasu daga cikin Jami’an gwamnati da hannu. Irin wannan zargi dai ya sanya gwamnan jihar jigawa Umar Namadi dakatar da guda daga cikin kwamishinonin sa tare da bada umarnin gudanar da bincike akai.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a, wadda sakataren gwamnatin jihar Jigawa Alhaji Bala Ibrahim ya sanyawa hannu, gwamman jihar Umar Namadi, ya bada umarnin dakatar da kwamishinan ciniki da masana’antu Alhaji Aminu Kanta, bisa zargin sa da hannu a almundahana a tsarin aiwatar da Shirin gwamnatin jihar na ciyar da mabukata a wannan mawata na Ramadana.

Wni jagora a cikin jagororin kungiyoyin cigaban al’umma a jihar Jigawa, Comrade Salisu Mazge Gumel ya bibiyi yadda gwamnatin jihar ta Jigawa ke aiwatar da wannan Shirin na ciyarwa, la’akari da daruruwan miliyoyin naira da gwamnatin ta kebewa tsarin.

“Akwai kumbiya-kumbiya a cikin harkar, yanzu zaka abinda ake ba ko wacce mace shine kwano 10 na, gero,da kwano 10 na shinkafa, amma bubu wanda zai tsaya ya tabbatar da cewa, wannan adadi an dafa shi, baya ga haka ‘yan kwangilar dake rarraba kayan ga masu dafawar babu wanda zai sanya masa idanu ya tabbatar da cewa, ya bada adadin daya kamata ga masu dafawa.”

A jihar Kano ma dake makwaftaka da jihar ta Jigawan, irin wannan badakala gwamnan jihar Abba Kabiru Yusuf ya gano a tsarin ciyar da mabukata na gwamnatin sa a cikin wannan wata mai alfarma.

Kimanin naira biliyan biyu gwamnatin ta kebewa Shirin, amma a wata ziyarar ba zata gwamnan ya nuna rashin gamsuwa da nau’in abincin da ake baiwa talakawa.

Sanusi Bature Dawakin Tofa shine Daraktan yada labaru na gwamnan yace, “Mai girma gwamna ya kewaya da kansa daya daga cikin cibiyoyin da ake wannan aiki kuma ya ga abin da akeyi ya saba da umarnin daya bayar, wanda haka ta sanya ya bada umarnin cewa, tilas ne a canza wannan tsari kuma ayi bincike domin daukar mataki.”

Yanzu dai kusan makonni biyu kenan da suke shude har yanzu babu labarin dangane da irin matakin ladaftarwa da gwamnan ya dauka akan wadanda yace suna yi masa zagon kasa.

Dr Kabiru Sa’idu Sufi, mai sharhi akan harkokin gwamnati da lamuran yau da kullum yace, “Wannan yana nuna ta’azzara ne na cin hanci da rashawa da almundahana, musamman akan abubuwan da suka shafi ayyukan gwamnati.”

Wannan zargin almudahana a tsakanin Jami’an gwamnati na zuwa ne a dai-dai lokacin da ‘yan Najeriya kef ama da kalubalen tsadar rayuwa a fadin kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG