Accessibility links

Fada da ya barke tsakanin hausawa da yarbawa kwanakin baya wanda ya kaiga asarar dukiya mai dimbin yawa ya sa gwamnati ta rufe kasuwar.

Kwanakin baya wani mugun fada ya barke tsakanin 'yan kasuwa hausawa da yarbawa. Sayarda wake a kasuwar shi ne musabbabin tashin fadan. Yarbawa sun yi korafin cewa hausawa kadai ke samun waken daga arewa maso gabashin Najeriya kana su sayar masu da dan karan tsada.

Dama can akwai zaman tankiya tsakaninsu tun lokacin da 'yan Boko Haram suka kashe 'yan kasuwa yarbawa da suka je fataucin wake a wajejen Maiduguri. A wannan lokacin mutane goma sha hudu suka halaka. Wannan lamarin ya sa su yarbawa suka daina zuwa fataucin wake a yankin. To amma 'yan'uwansu hausawa suna samu ana turo masu wannan irin waken.

A kan haka ne yarbawan suka hushe fushinsu domin wai hausawa na kulla makarkashiya su kwace kasuwar kacokan. Da fada ya barke bangarorin biyu suka yi asarar dukiyoyi da raunata juna lamarin da ya sa dole gwamnatin jihar ta rufe kasuwar.

Bayan sasantawa da 'yan kasuwar gwamna Isiyaka Ajimobi na jihar ta Oyo ya sake bude babbar kasuwar ta Bodija a birnin Ibadan. Bayan ya bude kasuwar gwamnan ya roki hausawa da yarbawa su zauna lafiya da junansu. Ya godewa kwamishanan 'yansadar jihar Alhaji Indabawa da sarkin hausawa da hakiman yarbawa da sauran masu fada a ji.A jawabin gwamnan ya ce iyalan yarbawan da suka rasa rayukansu a Maiduguri za'a biyasu diyar nera miliyan talatin. Ya yiwa hausawa wadanda suka yi asarar kayansu a takaddamar da ta faru a kasuwar cewa gwanatinsa zata duba ta ga abun da za'a yi masu na taimako.

'Yan kasuwar sun yi murnar sake bude kasuwar domin rufeta ya jawo masu matsala da ma wadanda suka saba zuwa cin kasuwar. Shugaban 'yan kasuwar na bangaren yarbawa Olalekan Aziz da shugaban bangaren hausawa Alhaji Garba Umar duk sun nuna farin cikinsu game da sake bude kasuwar. Sun gamsu da matakan da gwamnan ya dauka. Sun yi alkawarin cigaba da harkokinsu cikin lumana ba tare da sake tada zaune tsaye ba.

Hassan Umar Tambuwal nada rahoto.

XS
SM
MD
LG