Accessibility links

Wata Makaranta A Borno Na Daukar Nauyin Marayu Kyauta

  • Ibrahim Garba

Tashin hankalin arewa maso gabashin Nijeriya ya haifar da marayu da dama

Wata makaranta mai zaman kanta da ke Borno na daukar nauyin marayu, musamman ma wadanda tashe-tashen hankulan yankin arewa maso gabashin kasar ya rutsa da su.

Wata makaranta mai zaman kanta a jihar Bornon Nijeriya ta dukufa wajen daukar nauyin dalibai marayu da harkokin iliminsu da na ci da sha da sutura a makarantar da kuma makarantu na gaba. Makarantar mai suna ‘Future Prowess Islamic’ a yanzu haka na da dalibai dari hudu da ashirin (420).

Wanda ya assasa makarantar, Barrister Zannan Mustapha ya gaya ma wakilinmu Haruna Dauda Biu cewa daga kudaden shigar da ya ke samu daga wasu gidajen kifi uku da yah aka. Ya ce da kudin da ake samu daga sayar da kifayen ake samun kudaden ciyarwa da tufatarwa da sauran bukatar dalibai marayu.


Umar Garba wani dalibin makarantar ne da ya ce ya yi shekaru biyar a makarantar. Ya tabbatar ma wakilinmu cewa makarantar ce ke daukar komai dinsa kamar yadda wani dalibi ma mai suna Abubakar Mustapha ya tabbatar. Haka zalika wasu daliban makarantar sun sami makarantu na gaba a wasu wurare. Barrister Zannan Mustapha ya ce tashe-tashen hankulan da ke faruwa a yankin arewa maso gabashin Nijeriya sun haifar da marayu da dama ta yadda cikin shekaru biyu da su ka gabata an sami marayu dubu da dari biyar (1,500).
XS
SM
MD
LG