Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Katsina Ya Isar Da Sakon Buhari Ga ‘Yan Najeriya


Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya mika sakon barka da sallah ga ‘yan Najeriya inda ya nanata godiyarsa ga ‘yan kasar bisa addu’o’in da suka yi ta masa.

Da yake jawabi bayan hawan sallah a jihar Katsina, gwamna Aminu Bello Masari, ya gabatar da sakon shugaban ‘kasa inda yace shugaban yace a isar da godiyarsa ga mutanen Katsina kan addu’o’in da suke yi masa, ganin yadda Allah ya amsa addu’ar mutanen Najeriya.

Tun da farko da yayi nasa jawabin mai martaba sarkin Katsina Alhaji Dakta Abdulmuminu Kabir Usman, ya yabawa gwamnatin jihar Katsina saboda maido da tsaffin malamai da ta yi bakin aiki. Inda ya bayyana muhimmancin matakin ilimin firamare mai zama ginshiki a rayuwa.

Shima anasa jawabin gwamna Masari ya nanata muhimmancin ilimin fimare, ya kuma yi kira ga al’umma da tsaffin malamai da sauran wadanda ke da ilimin koyarwa da su taimaka don ilimantar da yara a duk fadin jihar.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG