Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Da Kungiyar Kwadago Na Jayayya Kan Albashi


ADAMAWA: Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo
ADAMAWA: Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Kungiyar kwadago ta jihar Adamawa ta ce malaman firamare da jami’an kiwon lafiya matakin farko ba su anfana daga tallafin Naira Biliyan 9.5 da gwamnatin tarayya ta samar shekarar da ta gabata don rage bashin albashin da ma’aikata ke bin gwamnati jiha.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Adamawa Kwamrad Dauda Maina, ya furta haka lokacin da ya ke maida martini ga ikirarin sakataren gwamnatin jihar Adamawa Dakta Umar Bindir, na cewar albashin wata daya kacal malaman firamare ke bin gwamnatin jiha lokacin da ya ke magana kan kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a jawabinsa na ranar daya ga watan nan cewa gwamnatocin jihohi ba su da hujjar kasa biyan ma’aikata albashi.

Kungiyar kwadago, inji ta bakin shugaban ta gwamnati ta biya albashi ga ma’aikatan da suke karkashin ta kan kari a shekarar da ta gabata abin da ya rage shine na bashin alawus na kudin hutu na shekara biyu. Yayin da ma’aikatan kananan hukumomi, malaman firamare da jami’an kiwon lafiya mataki na farko ke bin bashin albashi na watanni hudu zuwa biyar.

Baya ga albashin watanni hudu da malaman firamaren jihar Adamawa ke bin gwamnati, rabon a yi wa malaman firamare karin girma tun 2008 da kuma rashin biyansu kudaden alawus na hutun shekara hudu inji shugaban kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Adamawa kwamarad Rodney Nathan.

Da yake magana kan tallafi da gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi a bara don rage hakkokin ma’aikata, shugaban kungiyar masu kabar fansho ta kasa reshen jihar Adamawa Kwamarad Samson Almuru, ya ce sun kai kokansu ga Allah Ubangiji saboda dukkan matakan da suka bi na ganin sun sami biyan bukata ya ci tura.

Wakilinmu Sanusi Adamu ya yi nazarin jawabin na shugaba Mohammadu Buhari da ya ce gwamnatocin jihohi ba su da hujjar kasa biyan ma’aikatansu albashi kalaman da mai yiwuwa yana iya jefa gwamnatoci da kungiyoyin kwadago cikin rudani nan gaba.

Saurari rahotan Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG