Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Na Zargin ‘Yan Awaren Kamaru Da Mamaye Makarantu Sama Da 50


'Yan Makranta A Kamaru
'Yan Makranta A Kamaru

Hukumomin Kamaru sun ce mayakan ‘yan aware sun karbe ikon sama da makarantu 50 a yankin rainon Ingila, lamarin da ake ganin zai iya mayar da hannun agogo baya, a kokarin da gwamnati ke yi na farfado da harkar ilimi a yankin a watan Satumba.

Jami’ai a kasar ta Kamaru sun ce mayakan suna amfani da makarantun ne a matsayin wajen buya daga dakarun kasar da kuma wajen horar da mambobinsu.

Shugaban hukumar samar da ilimi a yankin, Wilfred Wambeng Ndong, ya ce wannan lamari yana ta masu da hankali sosai.

“Muna da makarantu 48 da aka lalata, sannan akwai wasu 53 da mayakan na ‘yan aware suke zaune a cikinsu a yanzu haka. Dangane da abin da ya shafi malamai kuwa, ba mu da tabbacin inda sama da malamai dubu uku suke, domin ba sa zuwa makaranta.”

Ya kara da cewa, mai yiwuwa mafi aksarin malaman da suka bata, sun tsere zuwa yankin rainon Faransa ko kuma suna boye a cikin dazuka.

Shugaban hukumar ta ilimin ya kuma ce, adadin daliban da ke zuwa makaranta a yankin na rainon Ingila ya ragu daga 422,000 a shekarar 2017, zuwa 5,500 a wannan shekarar da muke cikin, kuma hakan ya fi faruwa ne a garuruwa da ke da tsaro kamar Bamenda da Nkambe.

Sai dai a wani martani da suka mayar ta kafar sada zumunta, ‘yan awaren, sun musanta zargin cewa sun mamaye makarantu, inda suka ce an tura su wuraren da ake tunanin sojoji za su kai mamaya ne.

Cikin shekaru biyun da suka gabata, mayakan ‘yan awaren kan kai hare-hare a makarantu da dama, inda har sukan sace malamai da ‘yan makaranta.

Sai dai Kwamandan dakarun gwamnati a arewa maso yammaci, Janaral Robbinson Agha, ya ce sojoji za su tabbatar duk makarantu suna da cikakken tsaro kafin nan da ranar 3 ga watan Satumba da za a koma wani sabon zangon karatu.

Ya kara da cewa sojojin za su kashe duk wani dan tawaye da ya ki ajiye makami ya mika wuya.

“An ba mu umurni daga sama na mu bi su har maboyarsu, ya zama dole mu kawo karshen wannan lamari, ba za mu lamunci mutane su rika fasa gada da kona makarantu ba.”

Gwamnatin Kamaru ta ce mayakan ‘yan awaren sun kona makarantu fiye da 130, yayin da ‘yan awaren su ma suke zargin dakarun da kona makarantun yayin da suke fatattakarsu daga inda suke boye. Ko da yake, sojojin sun musanta wannan zargi.

Shi dai wannan tashin hankalin da ke faruwa a yankin rainon Ingilan a Arewa maso yammacin kasar ta Kamaru, ya faro ne tun a shekarar2016, a lokacin da malamai da lauyoyi suka yi zanga zanga kan yadda harshen Faransanci da masu magana da harshen suka mamaye harkokin kasar wacce ke amfani da harsuna biyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG