Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Yi Duk Abin Da Za Ta Iya Don Kubutar Da Daliban Nuhu Bamalli - Atiku


Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar

Hukumomin kwalejin sun rufe makarantar bayan da suka umarci dalibai su tafi gida har sai lokacin da aka neme su.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi kira ga gwammatin kasar, da ta dauki duk matakin da ya kamata don ganin ta karbo daliban kwalejin kimiyya da fasaha na Nuhu Bamalli da ‘yan bindiga suka sace.

Da daren Alhamis ‘yan bindigar suka kwashe mutum takwas a kwalejin suka kashe dalibi daya sannan suka jikkata wani a makarantar wacce ke garin Zaria a jihar Kaduna.

“Ina mai bakin ciki da rahotannin da ke cewa an sake garkuwa da dalibai, wannan karon a kwalejin Nuhu Bamalli da ke Zaria a jihar Kaduna.” Atiku ya ce cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a.

“Gwamnati ta yi amfani da duk abin da take da shi wajen ganin an kubutar da daliban.”

Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da malamai biyu kamar yadda bayanai ke nunawa.

A cewar Atiku, wanda shi ya tsaya wa babban jam’iyyar adawa ta PDP takara a zaben shugaban kasa na 2019, “kamata ya yi a ce, an hango aukuwar harin don a kauce masa.”

“Amma yanzu tun da lamarin ya riga ya faru, akwai bukatar gwamnatin tarayya, ta jiha, jami’an tsaro da iyalan daliban da aka kama, su hada kai su yi aiki tukuru wajen ganin an kubutar da daliban.” Atiku ya ce.

A halin da ake ciki, hukumomin kwalejin sun rufe makarantar har sai yadda hali ya yi, bayan wannan hari.

Wata sanarwa da kwalejn ta fitar ta hannu jami’in yada labaranta, Mahmud Aliyu Kwarbai, ta umarci dukkan dalibai su tafi gida har sai lokacin da aka neme su.

“Amma ban da daliban da za su rubuta jarabawar IJMB, wacce jami’ar Ahmadu Bello Zaria za ta gudanar a ranar Talata 15 ga watan Yuni, 2021.”

XS
SM
MD
LG