Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Nan Kan Bakata, Duk Wanda Aka Gani Da AK-47 A Bindige Shi – Buhari


Shugaban Najeirya, Muhammadu Buhari (Instagram/ Muhammadu Buhari)

“A matsayina na Babban Kwamandan Dakarun Najeriya, aikina na farko shi ne, samar da tsaro a kasa da kare rayukan fararen hula.” In ji Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce umarnin da ya bayar na a harbe duk wanda aka gani da bindiga AK-47 ba bisa ka'ida ba, a harbe shi, na nan yana aiki.

A watan Maris da ya gabata, shugaban Najeriya ya fara ba da umarnin, inda ya yi kira ga jami’an tsaron kasar, da su harbe duk wanda aka gani yana rike da wannan bindiga ko wani makami makamancin hakan.

Buhari ya bayyana wadannan kalamai ne yayin da gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu yake mika kayan aiki ga rundunar ‘yan sandan jihar kamar yadda wata sanarwa da kakakin shugaban Femi Adesina ya fitar.

Shugaban na Najeriya na ziyarar kwana daya a jihar ta Leags, inda ya je don kaddamar da wasu ayyuka.

“A matsayina na Babban Kwamandan Dakarun Najeriya, aikina na farko shi ne samar da tsaro a kasa da kare rayukan fararen hula.” Buhari ya fada cikin sanarwar.

Ya kara da cewa, “duk da irin kalubalen da muke fuskanta, Ina so ‘yan Najeriya su san cewa, za mu samar da tsaro a kasar nan.”

A cewar Buhari, “duk kasar da ake kai hare-hare akan ‘yan sandanta da gine-ginenta, kas ace da ta dauki hanyar kassara kanta.”

XS
SM
MD
LG