Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Zata Yi Adalci da Sakamakon Binciken Rikicin Sojoji da 'Yan Shiya -Buhari


Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya tabatarwa kungiyoyin rajin kare hakkin bil Adama na kasa da kasa da na cikin Najeriya cewa gwamnatinsa zata dauki matakan da suka dace akan rahoton binciken rikicin sojoji da 'yan kungiyar shiya da Shaikh Ibrahim El-Zakzaky ke jagoranta

Yanzu dai shugaba Buhari yana nazari akan rahoton kafin ya bayyana wa duniya irin matakan da zai dauka nan gaba..

Shugaban ya rugunmi akidar kare hakkin bil Adama domin itace gimshikin gina dimokradiya.

Idan ba'a manta ba lokacin da rikicin ya auku cikin watan Disamban bara, Shugaba Buhari ya fada, yayinda yake fira da 'yan jarida, cewa yana jiran sakamakon binciken lamarin ne kafin ya san matakin da ya dace ya dauka.

Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky, shugaban kungiyar Shiya ta Najeriya
Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky, shugaban kungiyar Shiya ta Najeriya

Gwamnatin yanzu mai bin tsari da doka da oda ce saboda haka duk wani matakin da za'a dauka zai bi tsarin doka ne babu sani babu sabo.

Gwamnatin tarayya zata cigaba da yin aiki ta yadda zata dinga kare muradun kowa da kowa da zummar hana aukuwan irin abun da ya faru

XS
SM
MD
LG