Accessibility links

Gwamnatin Burundi Ta Kama Mutane Kan Kisan Gillar Kwanan Baya

  • Halima Djimrao-Kane

Gawarwakin mutane 36 da 'yan bindiga su ka budewa wuta a wata mashayar garin Gatumba

Shugaban kasar Burundi ya ce an kama wasu mutane da hannu a kisan mutum 36 a garin Gatumba

Shugaban kasar Burundi yace gwamnatinsa ta kama mutane da dama dangane da kisan gillar da aka yi ma mutane 36 a wata mashaya dake garin Gatumba, a bayan da ya lashi takobin kamo wadanda suka aikata wannan lamarin cikin wata guda.

A cikin hira ta musamman da yayi da Muryar Amurka a nan Washington, shugaba Pierre Nkurunziza yace wasu alkalai su na ci gaba da binciken wannan hari na ranar 18 ga watan Satumba.

‘Yan bindigar sun abka cikin wannan mashaya, suka umurci kowa da ya kwanta a kasa, suka bude musu wuta. Mr. Nkurunziza bai bayyana wadanda suka kitsa wannan harin ba. A can baya yace an yi amanna maharan sun tsallaka cikin kasar ne daga bakin iyakar kasar Kwango, kilomita biyar daga garin na Gatumba.

Haka kuma, shugaba Nkurunziza ya kare kokarin gwamnatinsa na kwantar da wutar fitina a kasar, yana mai cewa lamarin tsaro ya inganta tun hawansa kan mulki a shekarar 2005. Yace har yanzu ana ci gaba da fama da matsalar mallakin bindigogi na haramun a Kwango ta Kinshasa, kuma an kwace bindigogi akalla dubu 80 daga hannun fararen hula.

XS
SM
MD
LG