Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Gwamnatin Wuccin Gadin Libiya sun yi imanin cewa Gaddafi ya boya a kusa da kan iyakar Aljeriya


Tsohon Shugaban Libiya Moammar Gaddafi
Tsohon Shugaban Libiya Moammar Gaddafi

Jami’an gwamnatin wuccin gadin Libiya sun ce hukumar sojinta na

Jami’an gwamnatin wuccin gadin Libiya sun ce hukumar sojinta na kyautata zaton tsohon shugaba Moammar Gaddafi, ya boye a garin Ghadamis da ke kusa da kan iyakar Aljeriya a yammacin kasar.

Jami’an gwamnatin sun fadi yau Laraba cewa, sun yi imanin cewa Gaddafi na samin kariya daga kabilar Asbinawa. Tsohon Shugaban ya taba goyon bayan Asbinawa masu bore a arewacin Nijar, kuma daruruwan tsoffin dakarun tawayen Asbinawa sun taya shi yaki.

A baya jami’an gwamnatin wuccin gadin sun zaci Mr. Gaddafin ya labe ne a garin Bani Walid da ke kudu masu gabashin Tripoli, babban birnin kasar a sa’ilinda wasu rahotannin kuma ke nuna cewa yana boye ne a kudancin kasar. Ba a dai kara ganinsa ba, tun bayan da dakarun da ke adawa da shi su ka kwace Tripoli, babban birnin kasar a watan jiya.

Tsananin bada-kashi a garin Sirte da aka yi wa kawanya, ya hana dakarun gwamnatin wuccin gadin kutsawa cikin daya daga cikin wurare kalilan da su ka rage a hannun mayakan Mr. Gaddafi.

Mayakan Gwamnatin Wuccin Gadin sun ce sun kwace tashar jirgin ruwan birnin, to amman har yanzu magoya bayan Gaddafi ne ke rike da mafi yawan Sirte.

NATO ta ce kimanin fararen hula 200,000 da akasarinsu ke Sirte da Bani Walid, har yanzu su na fuskantar barazana daga dakarun Gaddafi.

XS
SM
MD
LG