Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Chadi Ta Gabatar Da Tattaunawar Kasa A Matsayin Matakin Farko Na Shirya Kada Kuri'a


Shugaban Rukon Kwaya Na Chadi Mahamat Idriss Deby
Shugaban Rukon Kwaya Na Chadi Mahamat Idriss Deby

Gwamnatin Chadi ta ce za ta gudanar da taron tattaunawa na kasa da za a fara daga ranar 20 ga watan Agusta, a wani mataki na sharar fagen gudanar da zabe kamar yadda shugaban rikon kwarya Mahamat Idriss Deby ya yi alkawari a lokacin da ya karbe mulkin kasar bayan mutuwar mahaifinsa.

WASHINGTON, D.C - Deby ya ayyana kansa a matsayin shugaban majalisar soji ta rikon kwarya a watan Afrilun 2021 bayan an kashe mahaifinsa Idriss Deby, wanda ya dade yana mulki, yayin da ya ziyarci sojojin da ke yaki da ‘yan tawaye a arewa.

Chadian President Idriss Deby Itno
Chadian President Idriss Deby Itno

Da farko majalisar ta ce za ta sa ido kan mika mulki na tsawon watanni 18 zuwa mulkin dimokradiyya, amma ba ta nuna alamar shirya zabe ba yayin da wa'adin ke karatowa.

Deby ya gabatar da tattaunawar kasa a matsayin matakin farko na shirya kada kuri'a.

Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby Da Shugaban Nijar Mohamed Bazoum
Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby Da Shugaban Nijar Mohamed Bazoum

An fara samun matsin lamba daga kungiyoyin adawa na kasar Chadi da abokan huldar kasar don ci gaba da tsarin mika mulki. Kasar Chadi kawa ce ga Faransa da sauran kasashen yammacin duniya a yakin da ake yi da masu kaifin kishin Islama a yankin Sahel na Afirka.

-Reuters

XS
SM
MD
LG