Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Za Ta Kara Lafiyar Kwakwalwa Cikin Tsarin Inshorar Lafiya Ta Kasa


Kamfanin magunguna na Johnson and Johnson

Gwamnatin Ghana za ta kara larurar kwakwalwa a cikin jerin rashin lafiya da suke amfana da inshorar lafiya ta kasa.

Sabon shugaban hukumar tsarin inshorar lafiya ta kasa Dakta Okoe Boye ne ya fadi hakan, yayin da wakilan kamfanin magunguna na Johnson and Johnson suka kai masa ziyarar taya murna, a ofishin hukumar dake birnin Accra na kasar Ghana.

Dakta Boye, ya ce hukumar ta bukaci bayanai daga hukumar kula da lafiyar kwakwalwa, kuma ta fara gudanar da bincike don tabbatar da yiwuwar kara lafiyar kwakwalwa a cikin jerin cututtukan da suke karkashin inshorar.

A halin yanzu, kimanin kashi 95 cikin 100 na cututtukan da ake yawan fama da su a Ghana, na cin gajiyar inshorar.

Masana lafiyar kwakwalwa a Ghana sun yi maraba da wannan hobbasa da gwamnati ta yi, domin sun jima suna kira ga hukumar da ta kara lafiyar kwakwalwa cikin tsarin inshorar.

Dakta Nasiba Tahir Swallah, likitar kwakwalwa kuma malama a jami’ar Musulunci dake Accra, ta ce hakan zai taimaka musu likitoci da masu fama da larurar kwakwalwa, domin za su iya zuwa asibiti ba tare da fargabar kudi ba, domin inshorar za ta dauki nauyinsu.

Dakta Asma’au Ayyub a nata bangaren ta nuna yadda inshorar za ta taimaka wajen kula da masu cutar damuwa, wacce a baya inshorar ba ta dauka.

Ba da jimawa ba gwamnati ta amince da cutar kansar yara guda hudu a cikin tsarin inshorar lafiyar, daga ciki akwai matsanancin sankarar jini da bargo. Har wa yau, hukumar na kan hanyar shigo da magungunan cutar borin jini nan ba da jimawa ba cikin tsarin.

Saurari cikakken rahoton Idriss Abdullah Bako cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Dubi ra’ayoyi

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG