Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Gombe ta Karbi Lamunin Nera Biliyan Talatin


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Gwamnatin jihar Gombe ta karbi lamunin nera biliyan talatain daga kasuwar hannayen jarin Najeriya.

Kasuwar hannayen jari ta ba gwamnatin jihar Gombe lamunin nera biliyan talatin.

Karbar lamunin da gwamnatin jihar Gombe tayi tasa an shiga musayar martani tsakanin gwamnatin da kungiyar dake da'awar girka gwamnatin adalci. Tun watan Oktoban shekarar 2012 gwamnatin ta shiga yarjejeniyar karbar bashin da kasuwar hannayen jari har ma ta karbi nera biliyan ashirin a matsayin kashi na farko. Kawo yanzu ana jirewa jihar nera miliyan dari hudu kowane wata daga kason da take samu daga gwamnatin tarayya.

Tsohon karamin ministan wutar lantarki Alhaji Murtala Aliyu ya nuna fargaban lamunin da yace za'a biya cikin tsawon shekara bakwai zai karawa jihar nauyin bashi. Yace ana so ne a karbi bashin da za'a gina abubuwan da talaka zai ji a jikinsa ba a dauki bashi a gina kwararo ko magudanar ruwa ba. Bashin ya karawa jihar nauyi.

A martanin da gwamnatin jihar ta mayar kwamishanan kudin jihar Hassan Muhammed yace hanyar amanar da gwamna Dankwambo yayi anfani da kashin farko, yanzu yana da hurumin ya koma ya karbo sauran kashin kudin nera biliyan goma.

Sai dai Murtala Aliyu na fargabar dacewar amsar sauran kashin. Yace akwai wasu ayyuka da aka soma ba'a kammalasu ba. Shin idan an karbo sauran bashin za'a yi anfani da shi ne a kammala ayyukan da aka soma ko za'a soma wasu sabbi ne. Yace ya kamata a fadawa talaka an karba masa bashi kuma ga abun da aka yi dashi.

Kodayake Murtala Aliyu ya amince akwai ayyukan da gwamnatin tayi amma yana shakkar abun da ya shiga aljuhu talaka. Misali yakamata a mayar da hankali akan gina kasuwa.

Junaidu Usman mai taimakawa gwamnan jihar akan yada labaru yace gwamnan jihar Dankwambo Talban Gombe shi ne iyan karshen adalci. Yace abun da aka yi anfani dashi wurin gina reshen jami'ar Gombe a Kumo ya kai abun da aka yi kwaskwarima dashi akan makarantar horas da malamai da aka mayar da ita jami'ar Gombe.

Ita ma kungiyar manoma ta jihar Gombe tace ta ga anfanin lamunin. Umar Abdullahi jagoran kungiyar yace an tonawa masu nomar rani rijiyoyin burtsatse an kuma basu famfo da garmomi. Ban da haka gwamnan yayi shirin gina wata babbar kasuwa ta anfanin gona wadda babu irinta a nahiyar Afirka. Har an kawowa kungiyar zanen sun duba sun gyara kuma sun mikawa gwamnatin.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG