Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Habasha Tayi Watsi da Zargin Yiwa Kabilar Oromia Kisan Gilla


Gatachew Reda, ministan labaran Habasha
Gatachew Reda, ministan labaran Habasha

Mahunkutar kasar Habasha sunyi watsi da wani rahoto mai shafi 61, da kungiyar nan mai kare hakkin bil adama da ake kira HUMAN RIGHT WATCH ta bada bayanin kashe mutane sama da 400 cikin watanni 7 da suka gabata a kasar ta Habasha,

Lokacin da 'yan kabilar Oromia suka tashi domin kare filayen da suka gada kakani da kakanni, da gwamnatin Habasha take son ta kwace domin fadada birnin Addis Ababa, mahukunta suka kwantar dasu da karfin bindiga.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar ya shaidawa Muryar Amurka cewa kungiyar da bata da cikakken bayani, ta yaya za a yi ta iya bada sahihin bayanin da take yi na kare hakkin bil adama a lardin na Oromia.

Kakakin gwamnatin kasar Getachew Reda yace hukumar kula da kare hakkin bil adama ta kasar ta fittar da nata rahoton adadin mutanen da suka mutu wanda yake kasa da abinda kungiyar HUMAN RIGHT WATCH ta bayar, kana ya soki kungiyar yana cewa ta je ta sake bincike kafin ta shiga barara abinda da bata da cikakken bayani akan sa.

Ita dai kungiyar Human Right Watch tasha fada tana karawa cewa sojojin sun sha harbin masu zanga-zanga a lardin na Oromia da harsashi mai kissa, kuma suna haka ne ba tare da ko sun gargadi masu zanga-zangar ba, ko kuma yin anfani da wata hanya ta daban na wargaza masu zanga-zanga.

Tace yawancin wadanda aka kashe dai ‘yan makaranta ne, ciki ko harda yara ‘yan kasa da shekaru 18.

XS
SM
MD
LG