Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Adamawa Ta Kafa Kwamitin Bincike Harin Michika


Nigeria Boko Haram
Nigeria Boko Haram

Yanzu haka hankula sun fara kwantawa a yankin Michika da Madagali dake arewacin jihar Adamawa, biyo bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a daren jiya lamarin da ya jawo hasarar rayuka da dukiya.

Tuni gwamnatin jihar ta kafa kwamitin binciken da zai duba irin asarar da aka yi, kamar yadda kwamishinan yada labarun jihar Ahmad Sajo ya bayyanawa Sashen Hausa.

Wannan na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki hudu a sake gudanar da zaben gwamna a wasu runfunan zabe na kananan hukumomin biyu.

A sanarwar da ta fitar, rundunan sojin Najeriya ta bakin mukaddashin kakakin rundunan Kanar Sagir Musa, tace sojojin Najeriya sun sami nasarar kashe da dama daga cikin mayakan da suka kai hari da kuma kwace wasu motocin mayakan.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul'ziz

Rahoton harin Michika-3:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG