Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Borno Ta Horas Da Wasu Matasa Akan Harkokin Tsaro


Matasan da aka horas a jihar Borno
Matasan da aka horas a jihar Borno

Gwamnatin jihar Borno ta horas da matasa 2900 akan harkokin tsaro da zasu yi aiki kafada da kafada da sauran jami’an tsaro a dukkan kananan hukumomin jihar

Gwamnatin jihar Borno ta horas da wasu matasa 2900 da zasu dinga samar da tsaro a dukkan kananan hukumomin jihar.

Gwamnan jihar Kashim Shettima shi ya kaddamar da shirin. Yace matasan zasu dinga samar da tsaro ne, kuma zasu rika yin aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro.

Matasan da aka horas zasu dinga sa ido ne akan makwaptan su. An umurci matasan cewa da zara sun ga wanda basu yadda dashi ba ko kuma wani abu su sanar da jami’an tsaro ba tare da bata wani lokaci ba.

Gwamnan ya kuma yabawa matasan akan irin kokarin da suka yi wajen taimakawa. Matasan sun yi alkawarin aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata.

Kwamishanan shari’a na jihar Alhaji Kaka Shehu Lawan ya kara yiwa matasan bayanin irin ayyukan da zasu yi da suka hada da bada taimakon gaggawa ga marasa lafiya

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG