Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Gombe Zata Hukunta Masu Karkata Taki


Taron manoma na kasa da kasa

Gwamnatin jihar Gombe zata hukunta masu karkata takin gwamnati zuwa kasuwa domin su sayar.

Gwamnatin jihar Gombe ta sha alwashin hukunta duk wanda aka kama yana karkata takin da gwamnati ta kawo domin jama'a zuwa kasuwa domin sayarwa. Ta ja kunne masu aikata irin wannan aika-aikar cewa zasu gwammace kidi da karatu idan suka fada hannun hukuma.

An yi gargadin ne yayin da ake kaddamar da bikin raba taki domin noman bana. Gwamnan jihar shi ya kaddamar da bikin. Ya ce takin na jama'a ne don haka ba za'a bari wasu su wawureshi ba domin cimma muradun kansu. Gwamnan jihar Dankwanbo ya ce bana an sayi taki tan dubu ashirin da garmar shanu dubu daya da dari daya da arba'in. Ya ce kowane buhun taki kudinsa nera dubu shida ne amma manoma masu karamin karfi zasu biya nera dubu uku kawaikowane buhu. Haka kuma gwamnati zata bada garma da shanu ga duk manoma.Ya roki mutanen Gombe su yi wa Allah su tabbatar da an yi adalci wurin rabo.

A nashi bayanin Kwamishanan Noma Dahiru Buban Biri ya ce a binciken da ya yi 'yan neman alfarma da makaryata su ne ke karkata takin zuwa kasuwa. Ya ce wani zai zo yana neman a bashi taki da sunan shi manomi ne amma da an bashi sai ya je ya sayar. Wasu 'yan siyasa sai su zo su matsa a basu da hakan ya faru sai su je su sayar. Yin hakan kuma rshin adalci ne ga al'umma. Shi kuwa mataimakin shugaban kungiyar manoma ta kasa Sanata Sa'idu Dan Sadau ya fadi dalilin da yasa mutane basa cin gajiyar taimakon da gwamnati ke yi. Ya ce mutanen da ake dora masu alhakin raba kayan daga sama har kasa basa yi da adalci.

Abdulwahab Mohammed nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG