Accessibility links

Kungiyar Daliban Musulman Najeriya Ta Nemi A Mayarda Shugaba Morsi

  • Ibrahim Garba

Matashi Musulmi

Kungiyar Daliban Musulman Najeriya ta Nemi a mayarda shugaba Morsi yayin da ta yi tur da juyin milkin da sojojin kasar Masar suka yi.

Kungiyar daliban Musulman Najeriya ta yi tur da juyin mulkin da sojojin kasar Masar suka yi inda ta nemi a mayarda zababban shugaban kasar kan karagar mulkinsa.

Mataimakin shugaban kungiyar ta kasa kuma shugaban kungiyar ta jihohin arewacin Najeriya Uztaz Yusuf Yakubu shi ya fada haka yayin da yake jawabi a birnin Ibadan na jihar Oyo jiya Lahadi. Ya ce kungiyar daliban Musulman Najeriya suna allawadai da hambare shugaban kasar Masar Mohammed Morsi da sojoji suka yi kuma suna kira a mayarda shi bisa ga karagar mulki domin shi ne zababban shugaban kasar. Ya ce wajibi ne su yi hakan. Ya ce kungiyarsu na goyon bayan 'yan'uwa Musulmai a Masar da duk wadanda suka tsaya a dawo da shugaba Morsi bisa ga matsayinsa na shugaban kasar Masar. Ya ce kodayeke basa kasar amma suna yi masu addu'a kuma su 'yan kasar su dage sai an mayarda shi shugaba Morsi. Ya kara da cewa haka aka yi a Algeria inda Musulmai suka ci zabe amma sai da aka cire shugaban. A kasar Falesdinu an yi haka inda Hamas ta ci zabe amma Amurka ta ce 'yan ta'ada ne. Yau ga shi an sake yi a Masar da goyon bayan Amurka da Isra'ila da magabayan Hosni Mubarak.

Wakilinmu ya tambayi Uztaz Yusuf ko yana da hujjar cewa Amurka ce ke bayan juyin mulkin. Sai ya ce idan bata da hannu ciki to me yasa bata dakatar da tallafin da take bawa sojojin kasar ba. Kuma kawo lokacin da yake magana shugaban Amurka bai ce komi ba ko kuma ya tilastawa sojojin su dawo da shugaba Morsi kan milkinsa. Ya ki ya yarda cewa sojojin sun yi haka ne domin su dakile wargajewar kasar. Ya ce 'yan koran Amurka da Isra'ila da El Barade da wasu su ne suka haddasa juyin mulkin.

Hassan Umar Tambuwal nada rahoto.

XS
SM
MD
LG