Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kori Malamai 233, Ta Na Shirin Yin Sabbin Jarabawar Kwarewa Ga Wasu 12,254


Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

"An kori malaman ne bayan gudanar da bincike a makarantu, jami’o’i da kwalejojin da suka ce sun yi karatu, inda aka gano cewa sun gabatar da takardun bogi ne ba su yi karatu a inda suka ce sun yi ba."

Gwamnatin jihar Kaduna ta kori malamai 233 daga aiki saboda zargin gabatar da takardun shaidar karatu na bogi a lokacin da aka dauke su aiki.

Shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar, Tijjani Abdullahi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ganawa da manema labarai a Kaduna.

Tijjani ya kara da cewa an kori malaman ne bayan gudanar da bincike a makarantu, jami’o’i da kwalejojin da suka ce sun yi karatu, inda aka gano cewa sun gabatar da takardun bogi ne ba su yi karatu a inda suka mika takardunsu ba kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.

Shugaban hukumar SUBEB din ya bayyana cewa an fara binciken ne daga watan Afrilun shekarar 2021 a matsayin wani bangare na aikin hukumar, na tabbatar da cewa dukkan malaman suna da cancantar kwarewar da suka gabatar.

A cewar Tijjani, babbar manufar gudanar da wannan shi ne tabbatar da cewa dukkan malaman makarantun jihar Kaduna suna da takardun shaidar kammala karatu da ake bukata kafin mutum ya yi koyarwa wadanda suka kunshi muhimman abubuwan da suka dace na aikin koyarwa.

Haka kuma, shugaban hukumar ta SUBEB na jihar Kaduna ya kara da cewa kawo yanzu an tantance takardun shaida na karatu 451 ta hanyar tuntubar hukumomin da suka bayar da takardar shaidar karatun, yayin da tara daga cikin cibiyoyin karatu 13 da aka tuntuba suka mayar da martani.

"Sai dai martani daga cibiyoyin karatu 9 sun yi nuni da cewa malamai 233 ne suka gabatar da takardun bogi wanda hakan ke wakiltar kaso 51 cikin 100 na takaddun shaida 451 wadanda aka sami amsa daga cibiyoyin karatun da suka bayar.

A cikin cibiyoyin karatun 9, wata cibiya daya tak ta nesanta kan ta daga ba da takardun shaidar kamalla karatu 212 daga cikin takardun shaida na bogi 233.

Hukumar SUBEB dai za ta kori malamai 233 da suka gabatar da wadannan takardun shaida na bogi, yayin da za'a mika takardunsu ga ma’aikatar shari’a domin fara gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya.

Kazalika, hukumar za ta ci gaba da duba sahihancin takardun shaidar karatu da malamai ke bayarwa domin tabbatar da cewa ba'a bari mutanen da ke amfani da takardun shaidar kammala karatu na bogi sun rage kimar aikin koyarwa ba.

A wani bangare kuma, hukumar SUBEB ta ce a cikin aikinta na tabbatar da gaskiya, za ta sanya sunayen malamai 233 da aka samu da gabatar da takardun na bogi a shafin yanar gizon gwamnatin jihar Kaduna nan take.

Haka kuma hukumar ta sanar da cewa za ta sake gudanar da sabuwar jarrabawar cancanta ga malamai dubu 12,254 daga watan Janairun shekarar 2022 a wani bangare na ci gaba da tantance malaman ta domin inganta kansu da kuma samar da ingantaccen ilimi a jihar.

Idan dai ba a manta ba a shekarar 2017 ne gwamnatin jihar Kaduna ta dauki sabbin malamai dubu 25 aiki bayan ta kori wadanda ba su cancanta ba fiye da dubu 22 sakamakon gudanar da jarabawar duba cancantar aiki.

Sai dai malamin makaranta, Kabiru Abdul, ya ce kamata ya yi hukumar SUBEB da gwamnatin jihar Kaduna su sake nazari kan korar ma’aikatan sakamakon yiyuwar jami’o’i, kwalejoji ko kuma cibiyoyin karatun da aka tuntuba ba su yi aikin tantance takardun shaidar yadda da ya kamata ba.

XS
SM
MD
LG