Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Jihar Anambra Za Su Fara Zuwa Makaranta Ranar Asabar


Wasu daliban Najeriya a aji (Facebook/Ma'aikatar Ilimin Najeria)
Wasu daliban Najeriya a aji (Facebook/Ma'aikatar Ilimin Najeria)

A watan Yulin da ya gabata, IPOB ta ayyana umarnin zaman gida a kowacce ranar Litinin a jihar ta Anambra wanda ya fara aiki a watan Agusta.

Gwamnatin Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ta ayyana ranar Asabar a matsayin ranar zuwa makaranta.

Hakan a cewar hukumomin jihar dabara ce ta cike gibin rashin zuwa makaranta da dalibai ba sa yi ranar Litinin saboda umarnin da kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB ta ayyana na zama a gida a kowacce ranar Litinin.

Kwamishinan yada labarai na jihar Mista C. Don Adinuba ya ce daukan matakin ya zama dole lura da cewa akwai bukatar a kare lafiyar dalibai da malamai tare da tabbatar da cewa karatu a jihar bai fuskanci nakasu ba.

“Muna so dalibanmu su yi karatu gwargwadon hali a cikin yanayi na kwanciyar hankali. Wannan nasara ce ga dukkan masu ruwa da tsaki, wato su daliban, malamansu, shugabannin makarantu, iyaye da masu kulawa, masu gari, masu makarantu, da hattaita kanta gwamnati.

“Ba ma so wani abu ya faru da 'ya'yanmu ko kuma malaman. Wannan shi ne martaninmu ga rikicin da muka tsinci kanmu a ciki." Adinuba ya kara da cewa.

Wannan mataki a cewar hukumomin jihar na wucin gadi kafin al’amura su daidaita.

Wannan lamarin dai ya ja hankalin jama'a sosai, ciki har da wani magidanci Mista Sunday Nwuka.

"Ina son hakan da yake ana zaman gida a kowace Litinin. A maimakon yara su rika zaman banza ba su koyi komai ba a ranar Litinin din, ai zuwa makaranta ranar Asabar ya yi.” In ji Nwuka.

Sai dai duk da cewa wasu na maraba da matakin wasu ba su yi na’am da shi ba.

"A matsayina na malama, wannan wahala ce sosai garemu, tun da za mu hada shi ne da lokutan darasi na musamman. Saboda haka, koyar da yara daga safe zuwa yamma ranar Asabar zai wahalar da mu sosai, amma za mu bar abin haka, don mu ci karfin darusan da muke koyarwa, kuma yaran su karu." Malamr makaranta Paulina Okoro ta ce.

A watan Yulin da ya gabata, IPOB ta ayyana umarnin zaman gida a kowacce ranar Litinin a jihar ta Anambra wanda ya fara aiki a watan Agusta.

Hukumomi a jihohin da ke kudu maso gabashin Najeriya na fatan yin amfani da wannan tsari idan har ya yi tasiri.

XS
SM
MD
LG