Accessibility links

Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Bada Gudumawar Samada Naira Milyan 70 Ga Iyalan Jami'an Tsaro

  • Aliyu Imam

Wata mace ake baiwa baki a binne danginta.

Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Alma'kura ya baiwa iyalan jami'an tsaro da aka kashe a rikicin Eggon tallafin samada Naira milyan 70, domin su shirya jana'izarsu da kuma kula da waddanda aka bari a baya.

Sakatariyar gwamnatin a jihar Nasarawa Hajiya Zainab Abdulmumini, tace, sakamakon kuka da iyakan jami'an tsaron suka kaiwa Gwamna Almakura kan matsalar jana'iza da kula da yara, gwamnan ya yanke shawarar baiwa ko wani iyali Naira milyan daya.
Akwai fiye da jami'an tsaro 70 daga hukumomi daban daban da wannan al'amari ya shafa.

XS
SM
MD
LG