Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kaduna Ba Za Ta Halarci Taron Sasantawa Da Kungiyar Kwadago Ba - El-Rufai


Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sam ba za ta karba gayyatar gwamnatin tarayya na zaman sasantawa da kungiyar kwadago ba.

A wani jawabi ta gidan talabijin mallakar gwamnatin kasar wato NTA, Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce ba wani jami’in gwamnatin jihar da zai tashi zuwa Abuja, domin halartar zaman na sasantawa da gwamnatin tarayya ta shirya da kungiyar kwadago.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yana mai nuni da cewa ba a maido da wutar lantarki ba, wanda ake gani sharadi ne da za a cika idan har za su halarci taron.

Kungiyar kwadagon ta kasa ta kwashe tsawo kwanaki 3 tana gudanar da yajin aiki na gargadi, domin kalubalantar korar dimbin ma’aikata da gwamnatin jihar ta Kaduna ta yi.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)

Yajin aikin ya gurgunta kusan dukkan lamurran rayuwa da na tattalin arziki a jihar, ciki kuwa har da yanke jihar daga layin wutar lantarki.

A cikin jawabin na sa, Malam El-Rufai ya ce “ta yaya wani jami’in jihar Kaduna zai halarci wani taro da gwamnatin tarayya ko kungiyar kwadago alhali jama’ar jihar ba su da wutar lantarki?”

Gwamnan ya zargi gwamnatin tarayyar da kasawa wajen gwada karfin ikonta akan kamfanin samar da wutar lantarki na kasa TCN, wanda ya kai ga kungiyar kwadago yin amfani da shi domin gurgunta al’amura a lokacin yajin aikin.

Kalaman na El-Rufai na zuwa ne bayan da kungiyar kwadagon ta janye yajin aikin, sakamakon sa baki da Ministan kwadago Chris Ngige yayi, tare kuma da gayyatar gwamnatin ta Kaduna da kungiyar kwadago domin wani taron gaggawa na sasantawa a yau Alhamis.

To sai dai kuma a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, kamfanin na samar da wutar lantarki na kasa ya ce tuni da ya sake maida wutar lantarki a jihar sakamakon janye yajin aikin, a yayin da kuma kamfanin rarraba wutar na KAEDCO ya bayyana shirinsa na hada wutar lantarkin.

XS
SM
MD
LG