Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kaduna Ta Ankarar Da Mutane Cewa Miyagun Iri Sun Shuka Nakiyoyi A Sassan Jihar


Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Gwamnatin jihar kaduna ta bukaci jama’a su yi kaffa-kaffa wajen hada-hadar su ta yau da kullum don a na fargabar miyagun iri sun shuka nakiyoyi a sassan jihar.

ABUJA, NIGERIA- Gwamnatin ta bayyana haka ne, biyo bayan fashewar wani bam a yankin karamar hukumar Kabala ta kudu a jihar Kaduna a ranar Lahadi, 27 ga watan Fubrairu 2022.

Kwamishinan tsaro da lamuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana wannan ankararwa a sanarwar da ya fitar.

Sanarwar ta ce an shuka nakiyoyin a sassan taruwar jama’a irin makarantu, asibitoci, hotel-hotel, gidajen barasa, filayen shakatawa, gidajen abinci, tashoshin mota da wajajen ibada.

Gwamnatin ta bukaci masu fasa dutse su yi takatsantsan a filayen aikin su da gujewa barin nakiyoyin su fada hannun miyagun iri.

Hakanan sanarwar ta bukaci mutane su kai labarun wadanda ba su yarda da take-taken su ba ga jami’an tsaro, inda har a ka ba da lambobin waya da za a kira don ba da sanarwar gaggawa.

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG