Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kamaru Ta Yankewa Bangaren Ingilishi Yanar Gizo


Gwamnatin kasar jamhuriyar Kamaru ta yankewa bangaren ‘yan waren kasar masu amfami da harshen Ingilishi yanar gizo, kuma ta kara yawan jami’an tsaro a sashin yayin da suke yunkurin kafa tutar su.

Alhaji dan’asabe shine Kakakin bangaren da ke neman a ware masu amfani da harshen Ingilishi ya bayyanawa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Awal Garba dalilin sun a neman yankewa daga bangaren

Ya ce “tunda gwamanti ta dauki wadannan matakai na tura sojoji a wannan sashi, ya nuna cewa tada kayar bayan da jama’ar bangaren suka yi akan garskiyar su ne, domin ba jahilai bane, suna ilimi dan haka kamata yayi a koma a binciki abinda tarihi ya ce musamman akan yarjejeniyar da aka yi tun daga tsahon shugaban kasar har ya zuwa yanzu”.

Ranar 1 ga watan Satumba, ‘yan awaren suka tsayar a matsayin ranar ‘yancin kai da kuma kafa sabuwar kasa domin fara amfani da sababbin takardun kudi da kuam kafa sabuwar tutar kasar da suka sawa suna Ambazoia.

Mamaye yawancin manyan guragen ayyuka da manyan mukamai da ‘yan bangaren masu amfani da harshen Faransa suka na daga cikin dalilan da suka sa ‘yan bangaren suka bukaci a ware.

Domin karin bayani, saurari cikakken rahoton Awal Garba a nan

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG