Fira Ministan Somalia Hassan Ali Khaire da shugaban rundunar sojin Turkiyya, Janar Hulusi Akar sun kaddamar da sasanin soji mafi girma da Turkiyya ta gina a Mogadishu.
Sansanin mai tsawon kilomita hudu, na dauke da dakunan kwanan sojoji da wurin horo da na motsa jiki.
An kwashe shekaru biyu ana gina wannan sansanin wanda aka kaddamar da shi a jiya Asabar.
A cewar Janar Akar, bude wannan sansanin, alama ce da ke nuna yadda kasar Turkiyya ta himmatu wajen taimakawa Somalia.
Fira Minista Khaire ana shi bangaren ya ce, bude sansanin wata alama ce da ke nuna cewa Somalia ta dauki hanyar kare kanta.
Sama da dakarun Turkiyya 200 za su horar da takwarorinsu na Somalia kusan 1,500, a cewar ma’aikatar tsaron Somalia a wannan sansanin.
Facebook Forum