Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kasar Burkina Faso na Neman Kawo Karshen Takaita Shugabancin Kasar ga Wa'adi Biyu


Shugaba Blaise Compaore na kasar Burkina Faso.

Gwamnatin kasar Burkina Faso ta kaddamar da wani kokarin neman kawo karshen takaita shugabancin kasar ga wa'adi biyu.

Ministan cikin gidan kasar ya fada a jiya Talata cewa gwamnatin za ta gabatarwa da majalisar dokoki wani shirin dokar wanda zai bukaci a yi zaben raba gardama a akan batun na wa'adin mulki.

Magoya bayan shugaba Blaise Compaore wanda ya dade ya na mulkin kasar ne suka yi matsi lambar samar da sauye-sauyen domin ya samu damar sake tsayawa zaben shekara mai zuwa idan ya gama wa'adin mulkin shi na biyu.

Amma madugun 'yan adawa Benewende Stanislas Sankara ya ce za su yaki zaben raba gardamar da ake son yi,

Benewende Stanislas Sankara ya ce idan ya zama wajibi, 'yan adawa za su bijirewa dokokin kasa.

Blaise Compaore dan shekaru 63 ne ke mulkin kasar Burkina Faso tun shekarar 1987 da ya yiwa aminin shi juyin mulki.

Ya lashe zabubbukan shugaban kasa a shekarun 2005 da 2010 bayan da wata kotun kundin tsarin mulkin ta yanke hukuncin cewa matakin takaita shugabanci ga wa'adin mulki biyu da aka gabatar a shekarar 2000 bai shafi shugaban da dama ya na mulki kafin dokar.

Kafin shirin dokar neman yin zaben raba gardamar ya samu shiga, dole ne shugaban kasar da abolan mulkin shi su samu kuri'u masu rinjaye a majalisar dokokin kasar mai kujeru 127.

Jam'iyar shi ta CDP ta samu kujeru 70 a zaben shekarar 2012, amma daga baya ta dandana kudarta saboda da yawa sun yi canjin shekar akan maganar yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima.

XS
SM
MD
LG