Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Na Daukar Matakan Dakile Karuwan Al'umma


Ma'aikaciyar kiwon lafiya

Yawan karuwar al’umma a Najeriya ta sama da kashi uku cikin dari a kowace shekara, yasa hukumomin kasar suna bada magungunan tsaranta iyali a kyauta tare da bada nasiha ga iyalai a Najeriya domin rage karuwar al’umma.

Kasar Najeriya da tafi kowace kasa yawa al’umma a nahiyar Afrika, anasa ran yawan al’ummarta zai kai miliyon dari hudu kafin shekarar 2050, adadin da zai ninka yawan al’ummar ta yanzu, a cewar hukumar kididdigar al’umma ta Amurka

Aure da wuri da yawan haifuwa da kuma rashin samun magungunan tsaranta haifuwa suna cikin manyan dalilan dake kara yawan al’umma a Najeriya. Haka zalika batun al’adu da na addinin suke taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.

Wani dan fafutukar tsara rayuwar iyali Ejike Orji ya bayyana damuwarsa a kan yanda ake samun karuwar al’umma ba tare da daukar kwarar matakan dakile hakan ba.

Yace muna sanun karuwar al’umma cikin gaggawa fiye da ci gaba da muke samu. Yace wannan ne kuma babban dalilin da yasa Najeriya ta zama daya a cikin kasashe mafi yawan talakawa a duniya.

Amma wannan lamari zai iya sauyawa. Wani aikin fafutukar rage haifuwa na wata kungiya mai zaman kanta ta Planned Parenthood Federation of Nigeria, yana bada nau’in tsarin haifuwa da dama tare da bada shawara a fadin kasar..

Aikin hadin gwiwar tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar mai zaman kanta yana samun nasara a cewar kungiyar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG