Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Sha Alwashin Kin Biyan Duk Ma'aikacin Da Ya Shiga Yajin Aiki


Gwanatin tarayyar Najeriya, ta ce daga yanzu duk ma’aikacin da ya shiga yajin aiki, bazata biya shi albashi ba bisa la’akari da dokar kwadago ta 43, amma kungiyar kwadago ta Najeriya, ta bayyana cewa haka bazai taba yiwuwa ba.

Shugaban kungiyar ‘yan kwadago ta kasa Comrade Ayuba Wabba, ya bayyana cewa dokar tana nan amma bata da wani tasiri domin tsarin ya bayyana cewa ma’aikaci ba bawa bane, yana da ‘yanci ya nemi hakkin sa, shiyasa dokar taki ci taki cinyewa.

Barista Ali Arab, lauya ne mai zaman kansa a babban birnin tarayyar Najeriya, ya bayyana cewa dokar an tsara ta ne tsakanin mai aiki da mai daukar aiki, wato yarjejeniya kan wannan zai yi aiki daya bangaren kuma zai biya wanda ya yi aikin.

Ya kara da cewa dokar bat aba ma’aikaci hurumin tafiya yajin aiki haka nan kawai ba, akwai kuma inda ba a ba mai daukar aiki damar kin biyan ma’aikaci ba, ya danganta daga abinda suka zauna suka tsarawa kansu.

A bangaren ma’aikata kuwa da dama sun goyi bayan wannan doka yayinda wasu kuma ke anin akasin hakan.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG