Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Tilasta Yin Rigakafin Koronabirus Ga Duk Ma'aikatanta


Sakataran Gwamnatin Tarayyar Najeriya Mr. Boss Mustapha
Sakataran Gwamnatin Tarayyar Najeriya Mr. Boss Mustapha

Gwamnatin tarrayar Najeriya za ta soma aiwatar da shirin tilastawa dukan ma'aikatan gwamnati da ke karkashin tsarin akbashinta, yin allurar rigakafi cutar koronabairos, ko kuma a dauki mataki akan su.

Wannan matakin zai soma aiki daga ranar 1 ga watan Disamban wannan shekara ta 2021, inda dukkan ma’aikata da ke karkashinta za su bayyana katin shedar karbar rigakafin cutar COVID-19 kafin su samu izinin shiga Ofisoshinsu na aiki.

Sakataren Gwamnatin Tarayya kana jagorar Kwamitin Shugaban Kasa kan yaki da cutar COVID-19 a kasar Boss Mustapha ya ce duk ma'aikacin da bai gabatar da shaidar allurar rigakafinsa ba, to dolle ne ya bayyana sakamakon gwajin cutar da aka yi masa cikin sa'o'i 72 a dukkan fadin kasar.

Gwamnati ta dauki matakin ne sakamakon alkaluman da aka samu a cikin makwanni hudu da suka gabata, da ke nuni da cewa ana samun raguwa a gwaje-gwajen da ake yi a wasu jihohi kan cutar yayin da na wasu ke hawa.

Ya zuwa yanzu mutane dubu 208,153 ne rahotanni suka nuna sun taba kamuwa da cutar, mutane 2,756 suka rasa rayukansu, yayin da kimanin mutane 195,936 suka warke daga cutar.

Boss Mustapha Ya ce jumlar gwajin cutar COVID-19 ga 'yan Najeriya ya tsaya a miliyan 3.14.

An dai samu rarrabuwar kawuna tsakanin yan kasar kan wannan sabon matakin na gwamnati, inda wasu suka amince da allurar rigakafin wasu ko har yanzu ba su aminta ba .

XS
SM
MD
LG