Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Tuhumi Kamfanin Binance Da Zargin Kin Biyan Haraji


BINANCE
BINANCE

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dauki matakin shari'a akan binance, wani fitaccen dandalin hada-hadar kudin kirifto

WASHINGTON DC - Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta Tarayya (FIRS) ta sanar da hakan, inda tace an shigar da tuhume-tuhumen ne a hukumance gaban babbar kotun Abuja a yau Litinin.

Karar dai na tuhumar dandalin Binance da zarge-zargen kaucewa biyan haraji guda 4.

A cikin kunshin wadanda ake tuhuma tare da Binance din akwai Shugabannin Kamfanin; Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla da yanzu haka ya tsere daga hannun Hukumar EFCC me yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati.

Tuhume-tuhumen da ake yiwa Binance sun hada da zargin: kin biyan harajin VAT da ake caza akan kowace hada-hada da wanda ake biya akan gudanar da kamfani da kaucewa bayar da bayanai akan harajin da kamfani ya kamata ya biya da kuma yin amfani da dandalin wajen taimakawa abokan huldarsa su kaucewa biyan haraji.

Har ila yau, gwamnatin tarayyar Najeriya na zargin Binance da kin yin rijistar kamfanin da hukumar FIRS a bisa dalilai na biyan haraji da kuma karya dokokin haraji na kasar.

Gwamnatin Tarayyar ta kuma jaddada aniyarta ta tabbatar da yin biyayya ga dokokin haraji tare da yakar rashin gaskiya a harkar hada-hadar kudin intanet na kirifto.

Doka ta baiwa hukumar FIRS damar bin diddigi da tattarawa da kuma bada bahasi akan dukkanin harajin da ake karba a madadin gwamnatin tarayya ta hanyar amfani da dokokin haraji na Najeriya.

A baya, kamfanin Binance yayi ikrarin karya dokokin yaki da halasta kudaden haram a kasar Amurka a farko-farkon shekarar 2023 abinda ya sabbaba masa biyan tarar zunzurutun kudi har dala bilyan 4 da milyan 300, domin samun sassaucin hukunci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG