Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Za Ta Bullo Da Wani Sabon Tsarin Karbar Haraji


Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Najeriya na shirin rage yawan harajin da gwamnatin tarayya da na jihohi ke karba daga sama da 60 zuwa kasa da 10, shugaban kwamitin sake fasalin harajin ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

WASHINGTON, D. C. - Za a bullo da sabon tsarin a wani bangare na sauye-sauyen da za a samu wajen gudanar da harkokin kasuwanci cikin sauki da kuma kara samun kudaden shiga.

Najeriya, kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, tana da kaso 10.8 cikin 100 na haraji da GDP, wanda daya ne daga cikin kasashe mafiya karancin wannan adadin a duniya, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin kasar dogaro da rancen kudi domin gudanar da kasafin kudin kasar.

Masu zuba jari sukan yi la’akari da yawan karbar haraji a Najeriya da kuma yawan hukumomin tattara kudaden shiga da wajen yin lissafin yawar tsadar yin kasuwanci da kuma yin dari dari da saka hannun jari.

Taiwo Oyedele, mai bai wa shugaba Bola Tinubu shawara kan sake fasalin haraji, ya shaida wa manema labarai cewa, Najeriya na da sama da haraji da nau'ukan haraji 60 a hukumance wadanda gwamnatocin tarayya da na jihohi da kananan hukumomi ke karba, da doka ta wajebta.

Ciki har da harajin da ba na hukuma ba, harajin da hukumomi ke karba bisa ka’ida ko wadanda basa bisa ka’ida, ba ba tare da goyon bayan doka ba. Najeriya na da nau'ukan haraji sama da 200, in ji Oyedele, inda ya kara da cewa wannan adadi mai yawa yana sanya rayuwa cikin wahala.

“Gwargwadon yawan haraji, a gaskiya ma, gwargwadon karancin kudaden shiga da ake iya tarawa, saboda kawai yana janyo salwantar wasu kudaden, da kuma wasu mazambata da ba na gwamnati ba suna karbar kudi don amfanar kansu.” Inji shi.

Oyedele ya ce wani bangare na garambawul din zai ga sauye-sauye masu nasaba da kundin tsarin mulkin kasar domin fayyace ko wace hukumar gwamnati ce ya kamata ya karbi haraji iri kaza.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG