Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Za Ta Rufe Kamfanonin Ba Da Rancen Kudi Da Suka Saba Kai'da


Shugaba Buhari, dama, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, hagu

Hukumar kare hakkin masu sayayya ta Najeriya wato FCCPC ta bayyana cewa kwamitin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya ta kafa domin magance tauye hakkin mabukata da rashin adalci a masana’antar ba da rancen kudi za ta rufe sana’o’in masu ba da rance ba bisa ka’ida ba.

Hukumar FCCPC za ta fara aikin harkokin rufe sana’ar ba da rance da ake yi ba bisa ka’ida ba nan ba da jimawa ba a.

Babban jami’in hukumar ta FCCPC, Babatunde Irukera ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya wato NAN a ranar Lahadi a birnin Abuja.

Idan ana iya tunawa, a farkon watan Nuwamban shekarar nan ta 2021 ne gwamnatin tarayya ta soma aikin duba wasu haramtattun ayuka da kuma rashin adalci a cikin harkar bayar da lamuni na masana’antar ba da rance, tare da kafa kwamitin hadin gwiwa don shawo kan lamarin.

Ana sa ran kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa da ya karbi wasikun koke ta na’ura sama da 500 da bayanai game da binciken, zai jagoranci kokarin magance wasu dabi'un da za su iya haifar da rashin tabbas ga wasu masu ba da rance wadanda aka fi sani da loan sharks a turance.

Kwamitin hadin gwiwar ya kunshi wakilai daga hukumar FCCPC, babban bankin Najeriya wato CBN, hukumar yaki da cin Hanci da rashawa wato EFCC, hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA da hukumar kare hakkokin dan adam wato NHRC.

Irukera da ke zaman babban jami’in hukumar FCCPC, ya ce kwamitin zai kuma rubuta ka'idojin wucin gadi, wadanda ya zama wajibi kamfanonin bayar da lamuni na kudi su bi.

XS
SM
MD
LG