Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Neja Tana Nazarin Sabon Tsarin Albashi


NEJA: GWMNAN JIHAR NEJA Alhaji Abubakar Sani Bello

Gwamnan Jijhar Neja Abubakar Sani Bello yace yana nazari akan sabon tsarin albashi na naira dubu 30 da aka cimma yarjejeniya a tsakanin kungiyar kwadagon Nigeria da kuma gwamnatin Kasar,

A hira da manema Labarai a harabar majalisar dokokin jihar, gwamna Abubakar sani Bello yace abinda zasu iya yi shine zasu biya domin aikin gwamnati yana da yawa. Yace akwai ayyukan ci gaban sauran Jama ‘a kamar samar da ruwa, asibiti da dai sauransu. Yace dangane da batun karin albashi jihar Naija ta riga ta tsaida wannan shawarar tana jira ne kawai taji matsayin gwamnatin tarayya kafin ta fara aiwatarwa.

Gwamna Abubakar Sani Bello wanda yake magana bayan ya mika kasafin kudin shekara ta 2019 na sama da Naira Milyan Dubu 159 a gaban Majalisar Jihar, yace yana da kwarin guiwar cewa zasu samu kudadaen da suka kiyasta zasu samu a shekara mai zuwa.

Sai dai shugaban marassa rinjaye a majalisar Jihar Bello Agwara ya nuna rashin gamsuwa da yadda aka aiwatar da kasafin kudin shekara ta 2018.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG