Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Yanke Huldar Ayyukan Soja Da Jamhuriyar Benin


Fira Ministan gwamnatin Rikon kwaryan Jamhuriyar Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine
Fira Ministan gwamnatin Rikon kwaryan Jamhuriyar Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine

Gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar yanke yarjejeniyar ayyukan soja da jamhuriyar Benin sakamakon zargin makwabciyar kasar da saba alkawari.

Gwamnatin Nijar ta yi hakan ne bayan la’akari da yadda tace hukumomin Benin sun ba Faransa da CEDEAO hadin kai a shirinsu na afkawa sojojin da suka kifar da shugaba Mohamed Bazoum don mayar da shi kan mukaminsa. Sai dai masu sharhi sun gargadi kasashen biyu masu dadadden tarihi da su nuna halin dattako don warware komai cikin ruwan sanyi.

Sanarwar da kakakin Majalissar CNSP Colonel Major Abdourahmane Amadou ya karanta a kafar Gwamnatin Nijar na cewa, Jamhuriyar Benin ta bada izinin girke sojojin haya da kayan yaki a ci gaba da shirye-shiryen farmakin da Faransa ke son kawo wa Nijar da hadin gwiwar wasu kasashen CEDEAO, duk da yarjejeniyar ayyukan sojan da kasashen biyu suka cimma a ranar 11 ga watan Yulin 2022.

Ya kara da cewa Majalissar CNSP da gwamnatin rikon kwarya na jaddada niyarsu ta kaucewa aukuwar abinda ba zai yi kyau ba, bayan tunatarwa sau tarin yawa kan bukatar muhimmancin mutunta sharudan wannan yarjejeniya, sun yanke shawarar kawo karshen yarjejeniyar ayyukan soja ta ranar 11 ga watan Yulin 2022 kamar yadda yake a rubuce a sashenta na 23.

Tuni ‘yan Nijar suka fara bayyana matsayinsu akan wannan mataki da zai fara aiki a watanni shida masu zuwa. Dan fafutika na kungiyar ROADD Son Allah Dambaji, ya bayyana gamsuwa da abinda ya kira kare kai daga makiya.

Nijar da Benin masu al’umomi da al’adu guda na da dadaddiyar huldar kasuwanci, abinda ya sa kasashen biyu ke sauke odar hujjojin kasuwannin duniya a tashar jirgin ruwan Cotonou. Haka kuma An shiga wannan dambarwa a wani lokaci da ake gab da bude bututun man Nijar da ke ratsawa ta tashar jirgin ruwan SEME a kasar Benin, inda masani kan sha’anin tsaro da diflomasiya Moustapha Abdoulaye ya ja hankalin kasashen.

A watan yulin 2022 ne Nijar da Benin suka kulla yarjejeniyar ayyukan soja bayan la’akari da yaduwar ayyukan ta’addanci a kan iyakar kasashen biyu, to sai dai an shiga zaman marina sanadiyar juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023, kasancewar jamhuriyar Benin a sahun gaban kasashen da suka goyi bayan CEDEAO ta yi amfani da karfin soja don maido da hambararriyar gwamnati.

Rahotanni na cewa a yayin da Benin ta girke sojoji a garin Malanville na kan iyaka, haka ita ma Nijar a nata gefen ta aika da dakaru a garin Gaya.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Gwamnatin Nijar Ta Yanke Huldar Ayyukan Soja Da Jamhuriyar Benin.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG