Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijer Ta Kaddamar Da Shirin Bada Agajin Gaugawa Ga Miliyoyin 'Yan Kasar


Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta kaddamar da fasalin ayyukan agajin gaggawa domin wasu miliyoyin ‘yan kasar dake cikin matsanancin halin karancin cimaka da wadanda ke cikin halin  bukatar abinci mai gina jiki sakamakon farin da aka yi fama da shi a damanar da ta gabata.

Taron majalisar ministoci na karshen makon da ya gabata a karkashin jagorancin shugaba Mohamed Bazoum ne ya yanke shawarar soma zartar da matakan dake kunshe a fasalin agajin gaugawa wato Plan de soutien domin ‘yan kasar sama da million 6 dake cikin halin bukatar cimaka yayinda wasu sama da miliyan 2 ke bukatar abinci mai gina jiki sanadiyar farin da aka fuskanta a damanar da ta gabata.

Mai ba Firai ministan Nijer shawara a fannin ayyukan bunkasa noma Dr Haboubacar Manzo ya yi mana karin bayani game da mahimmancin daukan wannan mataki inda ya ce an yi tsarin ne saboda a shirya wa damina mai tahowa don a ba mutanen da ya kamata, a dinga bi ana kawo masu taimako akai-akai har lokacin da za a kai damina har zuwa bayanta, saboda a basu karfin gwiwa da kayan aikin don su tunkari wannan ranin du kuma abubbuwan da zai taimaka masu idan daminar ta taho.

Gardamar damana wani al’amari ne da ya zame wa jama’ar Nijer jiki saboda dalilai masu nasaba da illolin canjin yanayi abinda ya sa Shugaban kungiyar manoma da makiyaya ta Plate forme Paysanne Djibo Bagna ke ganin yanzu ilimi ya bamu dama, yanzu ana iya yin noma dukkan watanin goma sha biyu ba da wata matsala ba.

A irin wannan lokaci na neman hanyoyin tallafawa talakkawan da suka fada halin karin abinci hukumomin Nijer kan waiwayi kasashe masu hannu da shuni da kungiyoyin kasa da kasa domin su agaza.

A ra’ayin Diori Ibrahim na kungiyar Alternative mai kare hakkin jama’a a fannin cimaka, ya na ganin dole ne kasar ta canza tsari.

Noma da kiwo na kan gaba a ayyukan da jama’ar Nijer ke dogaro a kan su sai dai sannu a hankali wadanan fannoni na fuskantar koma baya a kowace shekara sanadiyar matsalolin canjin yanayi a kasar da tun fil azal ke fama da kwararowar hamada yayinda matsalolin tsaro a yankin tafkin Chadi da yankin Sahel suka takaita kai da kawowar manoma da makiyaya a wani lokacin da duniya gaba daya ta fada halin matsin tattalin arziki.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumini Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG