Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Oyo Za Ta Kafa Hukumar Sa Ido Akan Harkokin Makiyaya da Manoma


Gwamnan Oyo Abiola Ajimobi

Rikicin makiyaya da manoma da yake son zama ruwan dare gama gari a Najeriya ya sa gwamnatin jihar Oyo shirya taron neman zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu tare da sanar da kafa wata hukumar da za ta sa ido akan harkokinsu da kuma yin tanadin wurin kiwo.

A kokarin kawar da rikice rikice da samar da dawamammen zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a Oyo, gwamnatin jihar ta ce za ta kafa wata hukuma ta musamman da za ta sa ido ga harkokin bangarorin biyu.

Gwamnan jihar Sanata Abiola Ajimobi ya sanar da hakan a Ibadan babban birnin jihar a lokacin taron masu ruwa da tsaki a kiwo da noma da jami'an tsaro.

Gwamnan ya ce wajibi ne a kafa hukumar da za ta sanya ido lokaci zuwa lokaci ana zagayawa a duk fadin jihar domin tabbatar da cewa babu masu aikata laifuka kamar sace mutane ko sace shanu dake fakewa da sunan su makiyaya ne.

A cewar gwamnan za'a yiwa makiyaya da dabbobinsu rajista kuma duk makiyayin da aka kama dauke da makami za'a hukumtashi. Kazalika gwamnan ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na samar wa makiyaya wurin kiwo domin wanzar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.

Shi ma kwamishanan 'yan sandan jihar ya ce rikicin makiyaya da manoma da ya auku makwanni biyu da suka gabata ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara. Ya kira jama'a da su rungumi zaman lafiya su daina kashe kansu. Injishi jami'an tsaro zasu yi aikinsu babu tsoro babu ja da baya.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Bangarorin makiyaya da manoma su ma sun nemi da a zauna lafiya kana sun yiwa gwamnatin jihar Oyo godiya akan hada taron neman zaman lafiya tsakaninsu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG